Taskar Filfilon Dausayin Kauna (FDK) | Aminiya

Taskar Filfilon Dausayin Kauna (FDK)

Ya ku masu bibiya tare da aiko sakonni a wannan fili, ina muku gaisuwa tare da jinjinar jimirin bibiya. Haka kuma ina ba ku shawarar da ku rika turo sakonninku ta WhatssApp ko tes a lambar (08020968758) ko ta I-Mel, bashir@dailytrust.com Haka kuma ku rika sanya suna da adireshi da lambar waya a kasan sakon, idan kuma ba ku son a saka lambar wayarku a jarida, sai ku sanar. Har yanzu dai muna kara tambaya, wane gida kuke, GIDAN UWARGIDA FARIDA KO GIDAN AMARYA SARATU? Allah Ya sa mu dace. A wannan makon kuma ga wasu daga cikin sakonninku, kamar yadda aka saba:

 

Daga Usman Sarki Oil Rafin Dadi Katsina:

FDK, ina yi maka fatan alheri da fatan Allah ta’ala Shi kara wa wannan fili namu albarka, amin.

 

Daga A.B.A. Gangare Pandogari:

Assalamu alaikum FDK, da fatan kana cikin koshin lafiya. Allah Ya sa hakan, amin. A gaskiya muna nishadantuwa da wannan labarin na Uwargida Farida. Allah Ya kara basira, Allah Ya daga jaridar Aminiya, amin.

 

Daga K.S.K. Pandogari:

Assalamu alaikum. Ku saka zuciyoyinku cikin aminci kawai, ku kasance cikin so.

 

Daga Yusif A. Adam Abdullahi (09067851381):

Salam. Bayan gaisuwa mai tarin albarka ga ma’abota wannan shirin a duk inda suke. Jinjina ga FDK na Aminiya. A gaskiya ku na daban ne. Ina so ku taya ni addu’a, domin na kamu da son wata yarinya wacce ban taba ganinta ba amma na san mutunniyar kirki ce. Ina gaida masoyana, A’isha Gombe da abokina Isma’il Kano.

(To fa! Lallai soyayya ta kai maka karo, Malam Yusuf. A ce ba ka taba ganin yarinya ba, ba ka yi mu’amalar zahiri da ita ba amma har ka iya ba da shaidarta cewa ita ta kirki ce? Kodayake masu iya magana sun ce so hana ganin laifi. Ina taya ka addu’ar Allah ba da sa’a, Ya kadarta alheri a tsakaninku. – FDK).

 

Daga Yunus M. Saleh (08056333326):

Assalamu alaikum FDK, ina mika godiyata a gare ka tare da matukar nuna farin cikina mara misaltuwa ga ’yan uwa da abokan arziki. FDK, a dalilin wannan shafi na hadu da mutanen da ban san adadinsu ba. Kai in takaice maka, muna girmama juna sosai tare da kulla zumunci mai karfi. Sannan ba a iyakar wannan shafi muke tafka muhawara a kan rikicin su Farida ba, har a gidanmu ma musu muke yi da aunty ta. Ita ’yar jam’iyyar Saratu ce, ni kam ina bayan Hajiya Farida. FDK, ina maka godiya cikin carbi.

 

Daga Sabi’u Nura (08133388888):

Sallama a gare ka Malam FDK da sauran ma’abota wannan fili mai albarka. Gaskiya sunnanta gaskiya, ina  magana ne a kan Uwargida Ran Gida. Ina gaisuwa