Taskar Filfilon Dausayin Kauna (FDK) | Aminiya

Taskar Filfilon Dausayin Kauna (FDK)

    Bashir Yahuza Malumfashi

Ya ku masu bibiya tare da aiko sakonni a wannan fili, ina muku gaisuwa tare da jinjinar jimirin bibiya. Haka kuma ina ba ku shawarar da ku rika turo sakonninku ta WhatssApp ko tes a lambar (08020968758) ko ta I-Mel, bashir@dailytrust.com Haka kuma ku rika sanya suna da adireshi da lambar waya a kasan sakon, idan kuma ba ku son a saka lambar wayarku a jarida, sai ku sanar. Har yanzu dai muna kara tambaya, wane gida kuke, GIDAN UWARGIDA FARIDA KO GIDAN AMARYA SARATU? Allah Ya sa mu dace. A wannan makon kuma ga wasu daga cikin sakonninku, kamar yadda aka saba:

Daga Bashir Garba Dukamaje  (08167791483):

Assalamu alaikum Shugaba FDK, da fatar kana lafiya. Don Allah ina cigiyar ’yar uwata, wato Beauty ’Yarbaba Abuja, kauyen Gwagwa.

Musa Dangana Azare:

Assalamu alaikum FDK. Ina yi maka fatar alheri.

Daga Abdulmalik Kabir Ghude (08056717265):

Gaisuwa ga FDK da kuma sauran makaranta jaridar Aminiya. Gaisuwa gare ki Uwargida Farida. FDK, a gaskiya ta burge ni saboda gara ta nuna masa kuskurensa, don yana shugaba ya kamata ya sanar da ita, domin su tattauna. Ai ba za ta hana shi kara aure ba, su maza suna tunanin mata ba su kaunar kishiya; bayan ba haka ne ba, suna tsoron a kwaso masu alakakai ce, wadda ba kowane namiji ne ke ganewa ba. Saboda haka kada a ga laifin Farida!

 

Daga Rabilu Usman Kankara (08084902790):

Assalamu alaikum, FDK a gaskiya muna jin dadin wannan labari. Ni dai a gaskiya ina gidan Amarya Saratu, saboda shi namiji mijin mata hudu ne ba daya ba.

 

Daga Anas Hussain:

Assalamu alaikum FDK, Allah Ya kara daukaka da basira kuma Allah kara lafiya. Wallahi labarin nan yana sa ni nishadi amma gaskiya ina bangaren Uwargida Farida.

 

Daga Maman Zaid Kagarko:

Salam FDK, fatan alheri a gare ka. A gaskiya muna jin dadin wannan labari na Uwargida Farida. Allah Ya kara basira, Allah Ya daga jaridar Aminiya, amin. Ina bayan Uwargida Farida.

 

Daga KSK Pandogari (09075118294):

So mai saka mutum ya zauce. Kawai ka so mai sonka ya fi. Sannan ina farin ciki da wanan shafi na Dausayi Kauna da kuma fatar alheri ga daukacin magoya bayan wannan shafi. Wassalam!

 

Daga Aminu Ahmed Kanti Kazaure (09067962467):

Fatar Alheri ga Dausayin Kauna. Ni ma ina goyon bayan Alhaji Baba da ya kara aure amma ’yar mutunci, ba irin Saratu ba, wadda za ta rika kai shi wajen fati; domin namiji mijin mata hudu ne.

 

Daga Sabi’u Nura Maiduguri (08133388888):

Salam, gaisuwa mai tarin yawa a gare ka FDK, da sauran ’yan uwa maza da mata. Gaisuwa a kebe zuwa ga masoyiyata, wadda halinta daya da na Uwargida Farida, Sarautar Mata.

 

Daga Yusif Adam Abdullahi Kano (09067851381):

Salam, a gare ka nake suburbudo gaisuwa ga FDK, Aminiya da masu jimirin bibiyar wannan shirin a duk inda suke. FDK, ina son da nake wa bugon zuciyata ba zai musaltu ba. Ina mika gaisuwata ga masoyana, A’isha Gombe da abokina Isma’il Kano.