Taskar Filfilon Dausayin Kauna (FDK) | Aminiya

Taskar Filfilon Dausayin Kauna (FDK)

    Bashir Yahuza Malumfashi

Ya ku masu bibiya tare da aiko sakonni a wannan fili, ina muku gaisuwa tare da jinjinar jimirin bibiya. Haka kuma ina ba ku shawarar ku rika turo sakonninku ta WhatssApp ko tes a lambar (08020968758) ko ta I-Mel, bashir@dailytrust.com Haka kuma ku rika sanya suna da adireshi da lambar waya a kasan sakon, idan kuma ba ku son a saka lambar wayarku a jarida, sai ku sanar. Har yanzu dai muna kara tambaya, wane gida kuke, GIDAN UWARGIDA FARIDA KO GIDAN AMARYA SARATU? Allah Ya sa mu dace. A wannan makon kuma ga wasu daga cikin sakonninku, kamar yadda aka saba:

Daga Maryam Abdullahi Mati (08135108898):

Assalamu alaikum FDK, fatar alheri gare ka da ma’abota wannan fili. Ina bayan Uwargida Farida, domin kowace mace za ta so a kawo mata natsattsiyar mace, ba irin Saratu ba.

Daga Yayangida Yari Hadeja:

Muna tare da Uwargida Tankarin Gida Farida.

Daga Abdul Funtuwa (09017872733):

Bayan sallama irin ta addinin Musulunci, ina mika sakon gaisuwa ga sadauki, jarumin-jarumai wato FDK. Bayan haka, FDK ka mika mini sakon ban-gajiya ga masu bibiyar wannan jarida mai tarin albarka.

Daga Gimbiya Asma’u Kano

Assalam alaikum, FDK. Daukar ciki har sau biyu ga maza daban-daban a waje da Saratu ta yi ya nuna ba matar arziki ba ce, ‘mazinaciya’ ce. Ina gidanta a cikin wannan labarin don rage mata marasa aure amma watsattsiya ce, mara hankali.

Daga Y. Y Dantsoho Kaduna:

FDK, duk da cewa gidan Saratu nake don biyayya ga karin aure, yanzu ta bayyana ‘fatsika’ ce, mara natsuwa kuma ’yar-duniya. Yaya wani zai mata ciki ta zubar kuma yanzu ta kara daukar wani? Gaskiya akwai matsala a nan, zai yi wuya ta kasance mata ko uwa tagari, ma ji wanda ya yi mata cikin wannan karon da yardarta.

Daga Aminat Y. K. Abuja (08083736044):

Salam FDK, gaskiya ina bayan kawata Saratu Sarauniyyar Mata kuma ina cigiyar miji kamar Alhaji… Na gode.

Daga Samihat Ahmad:

Salam, babban yayanmu FDK, ina maka fatar alheri, ina Gidan Anty Farida. A mika mini gaisuwata zuwa ga babban yayana Isma’il Ali Kaduna da Hameed Fresh Boy.  Ku huta lafiya.

Daga Sulaiman Yahaya Kurkujan (08023142764):

Assalamu alaikum FDK, muna godiya da wannan fili mai albarka.

Daga Usman Sarki Oil Katsina (08032200026):

Assalamu alaikum FDK, a gaskiya muna nishadantuwa da nasihantuwa a cikin wannan fili naka mai cike da albarka. Allah Ya kara basira.

Daga Rabilu Usman Yangemen Kankara (08084902790):

FDK, fatar alheri a gare ka da ma duk masu bibiyar wannan shafi na Dausayin Kauna. A yau dai ina Gidan Alhaji Baba, ina goyon bayan ya kara aure amma ba Saratu ba saboda alamu sun nuna ba ta kirki ba ce, tunda har ta yarda da wani har ya yi mata ciki, wai don tana sonsa. Allah Ya kyauta, amin.

Daga Hameed Nura Fresh Boy:

Salam, barka FDK, ina fatar kana cikin koshin lafiya. Gaisuwa ta musamman ga jarumata A’ishat da fatar Allah Ya kare ta.