Daily Trust Aminiya - Taskar Filfilon Dausayin Kauna (FDK)
Subscribe

Taskar Filfilon Dausayin Kauna (FDK)

Ya ku masu bibiyar shafin nan a kowane mako, yau kuma ga wani sabon tsari da za mu jaraba, musamman dangane da wannan labari na Jidalin Kishiya: Labarin Farida. Ga dukkan alamu an samu rabuwar kai tsakanin masu goyon bayan Farida, wadanda ba su so Alhaji Baba ya yi mata kishiya. Wasu kuma suna tare da Saratu, suna so ta kasance amaryarsa. Daga yau za mu fara kuri’a, ku fara aiko da zabinku, tsakanin GIDAN FARIDA da GIDAN SARATU. Ma’ana, duk wanda zai turo sako, ya fara bayyana cewa, ina Gidan Farida ko kuma ina Gidan Saratu. Daga karshe, kafin kammala labarin nan za mu ga wadanda za su yi nasara a tsakani. Ga sakonninku na makon nan:

FDK namijin maza, Allah Ya kara kaifin basira, Ya kuma kare ka daga sharrin masu sharri da kai da abokan aikinka da ma duk wanda yake bibiyar wannan shafi mai tarin albarka. Bayan gaisuwa, don Allah ka ba ni dama in gaishe da amintacciyar zuciyata, wato Nafisat Dutsin-ma. Na gode, a huta lafiya.

Daga Aliyu Bala (07083773014):

Jinjina ta musamman gare ka FDK da fan alheri. Labarin Farida da Alhaji Baba yana sa ni nishadi sosai, godiya nake.

Daga Aliyu Bala:

Na ji dadin Labarin Malam Shagalalle. Allah Ya saka da alheri, Ya ba mu ikon gane gaskiya, amin.

Daga Umaima Idris Kagara:

Assalamu alaikum da fatan kuna lafiya. Ina yi maku fatan alheri, Allah Ya kare ku daga mahassadanku.

Daga Yakubu Kurma Zariya:

FDK, fatan alheri a gare ka, kai da sauran masu bibiyar wannan shafi mai albarka. Gaskiya muna jin dadin wannan labarin, Allah Ya kara basira amin. FDK, ka mika min sakon gaisuwa ga tauraruwata, masoyiyata Fatima Jibrin Jushi Zariya, fatan alheri a gare ki.

Daga Hameed Nura (Fresh Boy) Katsina (09067176209):

Sallama zan fara gare ka FDK, Allah Ya taimake ka da fatan kana cikin koshin lafiya.

Daga Sabi’u Nura Maiduguri (08133388888):

Ina miƙa saƙon gaisuwata a gare ka Malam FDK, Allah Ya ƙara basira da jinkiri mai amfani kuma ina gaida ’yar uwata, Hajiyata, Malamta wato A’isha Kastina.

Daga Khadija Abdullahi Abuja (08090968050):

Aminci ya tabbata a gare ku maza da mata da ke tare da mu a wannan shafi mai albarka. Ina gaishe da masoyana maza da mata kuma ina jinjina wa FDK. Allah Ya kara basira, a ci gaba da gashi. Gaskiya mutanen da suke bin bayan Alhaji Baba su yi la’akari da Saratu kuma su yi tunani shin wace ce Saratu? Haka kawai ba za ka ga mutum ba ka yi binkice a kansa ba ka yanke hukuncin aurensa. Saboda shi aure zaman gaskiya za a yi a cikinsa, wanda idan ba a yi bincike a cikinsa ba to za a tarar da matsala nan gaba. Saboda haka nake jan hankalinku da cewa mu tsaya mu ji wace ce Saratu sannan sai mu kwantar wa da Farida hankali.

Daga Bala B Oil Nasarawa-Abuja:

FDK, Allah Ya ba ka lafiya da nisan kwana, domin samun irinka a wannan lokacin yana da wahala, domin muna karuwa da wannan fili naka mai albarka. Sannan a mika min sakon gaisuwa ga Maryam Madawakin Jikamshi, Allah Ya sa a tashi lafiya.

Daga Yunus M. Saleh (08056333326):

FDK, ni fa ina goyon bayan (aunty) Farida, Allah Ya tsare ta kuma duk namiji mai hali irin na Alhaji Baba, ba na yi mai kallon mai adalci.

More Stories