✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Tattalin arzikin duniya zai fuskanci koma-baya a 2022 – Bankin Duniya

Hakan dai ya saba da harsashen da bankin ya yi tun da farko.

Bankin Duniya ya yi gargadin cewa tattalin arzikin duniya zai fuskanci koma-baya a shekarar 2022, sabanin harsashen da bankin ya yi a baya.

Bankin dai ya alakanta koma-bayan da ci gaba da bazuwar sabon samfurin COVID-19 na Omicron a sassan duniya daban-daban, lamarin da yake ci gaba da kawo hauhawar farashin kayayyaki da kuma raguwar samun kudaden shiga.

Hakan, a cewarsa, babbar barazana ce ga yunkurin da matsakaita da kananan kasashe ke yi wajen farfadowa daga annobar.

Sabon rahoton dai ya rage harsashen da bankin ya yi tun da farko na karuwar tattalin arzikin daga kaso 5.5 cikin 100 zuwa kaso 4.1 a shekarar ta 2022.

Tun farkon barkewar annobar dai, Bankin Duniya ya sha yin gargadi kan karuwar gibin da ake ci gaba da samu, musamman tsakanin manya da kananan kasashe.

Gwamnatocin kasashe kanana da dama dai na fuskantar karancin kudade, yayin da farashin kayayyaki ke ci gaba da hauhawa, masu kudi na kara kudancewa, talakawa kuma na dada shiga kangin talauci.

“Wannan karuwar gibin da ake fuskanta na da matukar sosa rai, musamman a kasashe masu tasowa saboda barazanar da hakan ke tattare da ita,” inji bankin.

Bankin dai ya ce rashin tabbas a sakamakon annobar COVID-19 samfurin Omicron din ne ke kawo cikas ga tattalin arzikin.