✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Kamfanonin mai 77 sun rike wa gwamnati N2.7 tiriliyan

Kudaden sun isa aiwatar da manyan ayyuka ko biyan basuka da ke cikin kasafin 2020.

Gwamnatin Tarayya na bin kamfanoni 77 na mai da iskar gas bashin Naira tiriliyan 2.7 na kudaden haraji da ba su biya ba.

Aminiya ta gano kudaden da kamfanonin suka rike sun isa Gwamnatin Tarayya ta aiwatar da manyan ayyuka ko biyan basuka da ke kunshe a kasafin kudin 2020.

Kudaden da kamfanonin suka rike wa gwamnatin sun hada da harajin riba da na sayayya (VAT) da sauran haraji da ya kamata su biya gwamnatin.

Babban Sakataren Hukumar Tabbatar da Gaskiya a Bangaren Ma’adinai (NEITI), Dokta Orji Ogbonnaya Orji, shi ne ya sanar da hakan a taron ’yan jarida na rabin shekara da hukumar ta gudanar.

Orji ya ce binciken da hukumar ta gudanar a kan basuka da gwamnati ke bin kamfanonin mai 77 ya tsaya ne a shekarar 2019.

“Rahoton binciken kudi da NEITI ta gudanar zuwa 2019 a bangaren mai da iskar gas ya nuna gwamnati na bin kamfanonin mai da iskar gas bashin Dala biliyan 6.48 wanda ya kai Naira tiriliyan biyu da biliyan dari shida da hamsin da tara a kan farashin Dala na yanzu, N410.35.”

Orji ya ce bayyana alkaluman na da muhimmanci a wannan lokaci da gwamnati ke neman kudaden shiga domin yi wa ’yan Najeriya ayyukan samar da ingantacciyar wutar lantarki da hanyoyi da ilimi da yaki da ta’adanci da kuma samar da ayyukan yi.