✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Tawagar WHO ta isa birnin Wuhan don gano asalin COVID-19

Tawagar kwarru da aka dora wa alhakin binciken gano tushen annobar coronavirus ta isa birnin Wuhan na kasar China inda cutar ta fara bulla. Kwararrun…

Tawagar kwarru da aka dora wa alhakin binciken gano tushen annobar coronavirus ta isa birnin Wuhan na kasar China inda cutar ta fara bulla.

Kwararrun na Hukumar Lafiya ta Duniya (WHO) sun isa birnin Wuhan ne a ranar Alhamis bayan sa-to-sa-katsin da ya kawo wa ziyarar tasu tarnaki.

Saukar masu binciken ke da wuya, aka yi musu gwajin cutar ta coronavirus sannan aka killace su sai bayan mako biyu.

Kwararrun za su yi aiki tare da masu binciken kimiyya na kasar China a aikin gano tushen kwayar halittar cutar.

A shekarar 2019 aka fara gano bakuwar kwayar coronavirus wadda ke haddasa cutar COVID-19 a birnin Wuhan na China.

Binciken gano asalin kwayar cutar na da hadari a siyasance, inda China ke gudun a dora mata laifin barkewar annobar COVID-19 da ta addabi duniya.

Amma masana kimiyya a kasar sun jima sun tababa ko a kasar cutar ta fara bulla, suna ganin akwai yiwuwar a wasu kasashen ta fara bulla kafin daga baya a gano ta Wuhan.

Sun ce alamun kwayar cutar da aka gano a kan wasu kayan kankara da aka shigo da su daga kasashen ketare na iya zama shaida cewa daga kasashen waje aka shigo da kwayar coronavirus a Wuhan.

Amma masu bincike na zargin jemagu daga yankin Kudancin China ne suka fara yada cutar.