✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Tayar jirgin saman Dana ta kama da wuta a Fatakwal

An dai samu ceto dukkan fasinjojin da ke cikin jirgin

An shiga yanayin fargaba a filin jirgin sama na kasa da ke Fatakwal a Jihar Ribas bayan tayar jirgin Dana da ke makare da fasinjojin Legas ta kama da wuta.

Jirgin dai na dauke da fasinjojin ne a kokarinsa na zuwa Legas.

Hakan ya sa jirgin bai samu damar tashi ba inda aka yi nasarar fitar da dukkanin fasinjoji 50 da suke cikin shi.

Kamfanin jirgin ya tabbatar da aukuwar lamarin a cikin wata sanarwa da take dauke da sa hannun Kakakin kamfanin, Kinsley Ezenwa ya bayyana.

Ya ce, “Jirginmu wanda zai je Jihar Legas a ranar biyu ga watan Mayu na shekara ta 2022 bai samu damar tashi ba saboda abun da ya da faru.

“Sai dai kuma an samu ceto dukkan fasinjoji 50 da ke cikin jirgin, za mu gudanar da bincike domin gano abin da ya haifar da wannan matsala, hakazalika muna ba wa dukkan fasinjojin da ke cikin jirgin hakurin soke tashin jirgin zuwa Jihar Legas,” inji sanarwar.