✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

‘Tazargade ka iya yin tasiri wajen maganin coronavirus’

Wasu masana harhada magunguna a najeriya sun ce akwai yiwuwar tazargade ta yi tasiri wajen kasha kwayoyin cutar coronavirus. Masanan na tofa albarkacin bakinsu ne…

Wasu masana harhada magunguna a najeriya sun ce akwai yiwuwar tazargade ta yi tasiri wajen kasha kwayoyin cutar coronavirus.

Masanan na tofa albarkacin bakinsu ne a kan umarnin da Shugaba Muhammadu Buhari ya bayar cewa a shigo da maganin da Madagascar ta hada wanda ta yi ikirarin cewa yana magance COVID-19.

An dai ce kasar ta Madagascar na amfani da wasu iytatuwa ne masu alaka da tazargade wajen hada maganin, wanda ta yi wa lakabi da COVID Organics.

Zainab Ujudud Sharif kwararriya ce a fannin harhada magunguna (wato Pharmacist a Turance) kuma ta shaida wa Aminiya cewa tun da dadewa binciken masana ya nuna cewa garin tazargade yana da tasiri wajen magance zazzabi.

A gargajiyance

“Mu da ma a gargajiyance muna amfani da tazargade a matsayin maganin zazzabi.

“Idan muka duba za mu ga cewa zazzabi yana cikin cututtukan da mai coronavirus ke fama da shi don haka idan aka yi amfani da tazargade zai taimaka kwarai da gaske”, inji ta.

Pharmacist Zainab ta kara da cewa, “Tun kimanin shekaru 100 da suka wuce kasar Sin ta gudanar da bincike a kan tazargade, inda ta gano cewa yana maganin zazzabin cizon sauro.

“Bayan da Hukumar Lafiya ta Dumiya (WHO) ta soke amfani da chloroquine sai aka fito da ACT wanda da tazargade ake  hada shi.

“Kuma a wannnan lokaci kasar ta China ke nomanta don haka ita take ba wa wani kamfani yake sarrafa ta yana yin wancan maganin zazzabin da shi”.

Sai dai ba ta wadata ba

Sai dai Pharmacist Zainab ta ce tazargaden da ke kasar nan ba shi da yawan da zai ishi mutane fiye da miliyan 180.

“Ba na mantawa a shekarar 2006 Shugaba Olusegun Obasanjo ya ce tun da maganin ACT yana da tsada to mu karbi ’ya’yan tazargaden daga China mu gwada shukawa a kasar nan, duk da cewa muna da tamu ta gargajiya.

“Mun shuka ta a jihohin Arewa da na Kudu. Amma wacce muka shuka a Arewa an fi samun sinadarin da ake nema a cikinta.

Yadda aka samu matsala

“Bayan mun kammala sai aka zo batun yadda za a sarrafa; to a nan aka samu matsala sakamakon canjin gwamnati – shi ke nan aka yi watsi da aikin.

“Wadda muka shuka din a baya sai muka mayar da ganyen ya zama ganyen shayi na tazargade. Tsakin kuma mutanen kauye suka rika turara shi a matsayin maganin sauro.

“Da a ce an ci gaba da wannan aikin to da sai dai mu ba wasu kasashen tazargade kamar yadda Madagascar ke yi a yanzu, domin lokaci daya muka fara nomanta da su.

“Amma kin ga da yake ba su dauki abin da wasa ba kin ga ai sun ci gaba da yinsa.

“Mu a yanzu buhu nawa muke da shi na tazargaden da za ta wadaci Najeriya? Babu.

“Kuma sakacinmu ne ya jawo mana hakan”, inji Pharmacist Zainab Ujudud Shariff.

Da yake sanar da umarnin shugaban kasar dai, Sakataren Gwamnatin Tarayya, kuma shugaban kwamitin cika aikin yaki da COVID-19 a Najeriya, Boss Mustapha, y ace sai an gudanar da Karin bincike a kan maganin na Madagascar idan an kawo shi.