✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Tegina: Dalibai biyu sun tsere daga hannun ’yan bindiga

Daya yarinyar tana asibiti kuma kamar ta samu tabin kwakwalwa.

Bayanai sun ce wasu karin dalibai biyu na Makarantar Islamiyyar Salihu Tanko da ke garin Tegina a Jihar Neja, sun tsere daga hannun ’yan bindiga.

Daliban biyu da suka kubuta na daga cikin fiye da dalibai 100 da ’yan bindiga suka sace fiye da tsawon wata guda.

Shugaban makarantar, Malam Abubakar Alhassan wanda ya tabbatar da hakan gas ashen Hausa na BBC, ya ce daliban da suka kubutu a yanzu mata wadanda suka samu nasarar sabewa daga cikin barayin lokacin da aka sace su.

A cewarsa, tun a wancan lokaci, sai yanzu Mai Duka ya kaddari dawowar yaran gida, inda daya daga cikinsu ta fara samun tabuwar hankali.

“Yarinya daya ce ta fara dawo wa kafin kuma sake samun ta biyun.

“Daya yarinyar tana asibiti kuma kamar ta samu tabin kwakwalwa domin ta kasa gane gidansu,” a cewarsa.

Aminiya ta ruwaito cewa, makonni biyu da suka gabata ne kimanin mutum 15 daga cikin wadanda ’yan bindiga suka yi garkuwa da su a garin Tegina na Jihar Neja suka kubuta.

Wakilinmu ya ruwaito cewa, mutanen sun tsere daga hannun masu garkuwar ne a yayin da masu tsaronsu suka bige da bacci bayan sun yi mankas da barasa.