✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Tegina: Mutum 15 sun tsere daga hannun ’yan bindiga

Sun tsere yayin da masu tsaronsu suka bige da bacci bayan sun bugu da barasa.

Rahotanni sun bayyana cewa, kimanin mutum 15 daga cikin wadanda ’yan bindiga suka yi garkuwa da su a garin Tegina na Jihar Neja sun kubuta.

Wakilinmu ya ruwaito cewa, mutanen sun tsere daga hannun masu garkuwar ne a yayin da masu tsaronsu suka bige da bacci bayan sun yi mankas da barasa.

Wadanda da suka tsere bayanai sun ce suna daga cikin mutanen da aka sace tare da dalibai 156 na Makarantar Islamiyyar Salihu Tanko da ke garin Tegina da ’yan bindiga suka kai wa hari a watan Mayun da ya gabata.

Majiyoyin rahoton sun ce mutanen da suka kubuta an raba su da sauran daliban Islamiyyar inda aka kai su wani daji a Jihar Zamfara.

Aminiya ta samu cewa, wadanda suka kubutar cikin sanda da kuma dabara suka bude kofar dakin da aka ajiye su a dajin yayin da masu gadinsu suka bige da bacci bayan sun yui mankas da barasa.

A makonnin da suka gabata ne gungun wasu ’yan bindiga suka farmaki Islamiyyar da ke garin Tegina, inda suka yi awon gaba da dama ciki har da dalibai yayin da suke tsaka da karatu.

Wasu rahotanni na nuni da cewa wadanda suka jagoranci sace daliban Jangebe a Jihar Zamfara ne suka yi garkuwa da daliban Islamiyyar na Jihar Neja.