✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

TETFUND zai raba fiye da N1bn ga manyan Makarantu a Najeriya

Jami'o'i, makarantun fasaha da Kwalejojin ilimi za su ci moriyar kudin.

Asusun Tallafawa Manyan Makarantu a Najeriya TETFUND zai raba wa manyan makarantun gaba da sakandire da ke fadin kasar tallafin naira 1,487,387,028 a bana.

Babban Sakataren TETFUND,  Mista Sonny Echone ne ya bayyana hakan a zauren tattaunawa da ya gudana ranar Litinin tare da shugabannin makarantun da za su ci moriyar kudin a Abuja.

Kamfanin Dillancin Labarai na kasa NAN ya ruwaito cewa kasafin kudin zai gudana a matakai 3, inda za a fara da jami’o’i, sai makarantun fasaha, sannan kwalejojin ilimi su biyo baya.

Haka kuma ya ce Shugaban Kasa Muhammadu Buhari ya ba da sahalewarsa akan biyan wadannan kudaden tallafin kamar yadda yake a kasafin asusun TETFUND na bana.

Echono ya ce rabon zai gudana ne kan tsarin daidaiton jihohi da yankunan mazabun Najeriya 3 kamar yadda doka ta shimfida.

Kamar yadda ya ambata, kowacce jami’a za ta samu naira 6,42,848,138, sai makarantun fasaha Naira 496,780,086, yayin da kuma kwalejojin ilimi za su samu Naira 447,758,804.

Sakataren na TETFUND ya ce kudaden tallafin na musamman za a sake su ga makarantun nan ba da jimawa ba.