✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Tikitin jirgin sama daga Abuja zuwa Kano ya sake kaiwa N135,000

Hakan ba ya rasa nasaba da tashin farashin man jirgi

Fasinjojin jirgin sama a Najeriya na ci gaba da kokawa kan tashin gwauron zabon da farashin tikiti ke ci gaba da yi, inda a yanzu ake biyan kusan N135,000 daga Abuja zuwa Kano.

Lamarin dai ya tilasta wa mutane da dama ko dai su soke tafiyar ko kuma su nemi wasu hanyoyin masu rangwame.

Kamfanonin jiragen sama dai na alakanta hakan da tsadar da man jirgin sama na Jet A1 da sauran harkokin gudanarwa suka yi.

Bara kamar yanzu dai, ana sayar da man ne a kan kasa da N200 kan kowacce lita, amma yanzu ya haura N800, kuma ana fargabar zai ma iya kaiwa N1,000 saboda rikicin Rasha da Ukraine.

Kazalika, dakatar da kamfanonin Aero Contractors da Dana da Hukumar Kula da Sufurin Jiragen Sama ta Kasa (NCAA) ta yi, ya taimaka wajen kara ta’azzara lamarin.

‘Babu tikitin kasa da N80,000 a yanzu’

Binciken Aminiya ya gano cewa kamfanonin jiragen da dama sun kara kudadensu, inda mafi karanci ya fara daga N80,000, a maimakon N50,000 a baya.

Wani fasinja da ya zanta da Aminiya ya ce ya shirya zuwa Legas daga Abuja don yin wani uzuri a ranar Alhamis din da ta gabata, amma jirgin kawai da ya samu shi ne na N125,000, kuma tilas ta sa ya hakura.

Kazalika, binciken da muka yi a ranar Larabar da ta gabata ya gano cewa kamfanin Ibom Air na cazar N78,000 daga Legas zuwa Abuja, kuma an saye galibin kujerun ma a hakan.

Shi kuwa kamfanin Air Peace na karbar N80,000 daga Legas zuwa Kano, amma kuma daga Abuja zuwa Kano, kamfanin Max na karbar N130,000.

Sai dai idan tun ana saura kwana biyu mutum ya yi tanadi, to N78,000 zai biya.

Bugu da kari, daga Legas zuwa Kaduna, kamfanin Azman na karbar N100,000, kodayake shi ya shafe tsawon makonni a haka.

Daga Legas zuwa Kano kuwa, farashin na kamawa daga tsakanin N95,000 zuwa N105,000, wanda yake danganta da lokacin da mutum ya biya.

Kamfanoni sun soke tikiti mai rangwame

Aminiya ta kuma gano cewa hatta kamfanonin da ake wa kallon masu tikitin rangwame irin na Green Africa, yanzu sun dakatar da shi, inda suke karbar kusan N80,000 daga Legas zuwa Abuja.

A baya dai, kamfanin kan sayar da tikitin Legas zuwa Abuja ne tsakanin N27,000 zuwa N35,000, a daidai lokacin da wasu ke karbar N50,000.

Daga Abuja zuwa Ilorin kuwa shi ma yanzu ya koma daga tsakanin N54,000 zuwa N70,000, a maimakon N25,000 a baya.

Ba laifinmu ba ne — Kamfanonin jiragen sama

Sai dai da yake zantawa da wakilinmu, wani masani kan harkar sufurin jiragen sama kuma shugaban kamfanin jirage na TopBrass, Kyaftin Roland Iyayi, ya ce tilas ce ta sa suka kara farashin don ya dace da yanayin da ake ciki.

Ya alakanta lamarin da tsadar man jirgi da sauran kayayyaki, inda ya ce dole sai sun yi hakan muddin suna son su ci gaba da kasuwanci.

Kyaftin Roland ya ce hanya daya tilo da gwamnati za ta taimaka farashin ya ragu ita ce ta shigo da man jirgin tare da sayar musu shi da sauki.