✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Sakamakwon Zaben Gwamnonin Najeriya Na 2023 (Alkaluma Daga:INEC)

Tilas mu maida martani idan Koriya ta Arewa ta harba makamin nukiliya —Amurka

Hukumar IAEA na zargin Koriya ta Arewa ta sake bude wata cibiyar makamai bayan an rufe ta a 2018

Mataimakiyar Sakataren Harkokin Wajen Amurka, Wendy Sherman, ta ce zai zame wa Amurka tilas ta maida martani idan Koriya ta Arewa ta kuskura ta aiwatar da gwajin makaminta na Nukiliya.

Jim kadan bayan ganawarsu da takwaranta na Koriya ta Arewa, Cho Hyun-dong a birnin Seoul, Sherman ta fada wa manema labarai cewa, “Duk wani gwajin makamin nukiliya da za a yi, saba wa yarjejeniyar Majalisar Dinkin Duniya ne, kuma za a maida martani ga gwajin makamin.”

Ana ci gaba da nuna fargabar cewar Koriya ta Arewa, wadda ta harba makamai masu linzami da dama a bana, na shirin gwajin makamin nukiliya a karon farko tun 2017.

A ranar Litinin sojojin Koriya ta Kudu da na Amurka suka harba makamai masu linzami guda takwas a gabar Tekun Gabashin Koriya ta Kudu, kwana guda bayan kasar ta harba wani makami mai linzami mai cin gajeren zango.

Hukumar Kula da Makamashin Nukiliya ta Duniya (IAEA) ta bayyana cewa, yunkurin da Koriya ta Arewa ta yi na fadada muhimman cibiyoyi a tasharta ta nukiliya da ke Yongbyon na ci gaba da bunkasa.

Bayanan Shugaban IAEA, Rafael Grossi, sun nuna  Koriya ta Arewa ta sake bude wata cibiyar makamai bayan an rufe ta a 2018, watakila don shirin gwajin makaminta na nukiliya.

“Gwajin makamin nukilya ya saba wa yarjejeniyar Majalisar Dinkin Duniya, kuma hakan zai haifar da fargaba,” inji Grossi.