✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Tinubu na taro da Gwamnonin APC sa’o’i bayan ayyana takarar Osinbajo

Taron na zuwa ne ’yam sa’o’i bayan Osinbajo ya ayyana takararsa

Jagoran jam’iyyar APC na kasa kuma tsohon Gwamnan Jihar Legas, Asiwaju Bola Tinubu, na taro da Gwamnonin jam’iyyar a ranar Litinin.

Taron, wanda ke gudana a masaukin Gwamnan Jihar Kebbi da ke unguwar Asokoro a Abuja, na zuwa ne ’yan sa’o’i bayan Mataimakin Shugaban Kasa, Farfesa Yemi Osinbajo ya ayyana tsayawa takara a zabe mai zuwa.

Daga cikin Gwamnonin da suke halartar taron har da na Kebbi (Atiku Bagudu) da na Jigawa (Badaru Abubakar) na Osun (Gboyega Oyetola) da na Legas (Babajide Sanwo-Olu) da na Filato (Simon Lalong) da na Kaduna (Nasiru El-rufa’i).

Da sanyin safiyar Litinin ce dai Farfesa Osinbajo ya bayyana aniyarsa ta tsayawa takarar a karkashin jam’iyyar APC a zabe mai zuwa.

Tun gabanin ayyana takarar tasa ma, Osinbajon shi ma ya karbi bakuncin wasu Gwamnonin APC domin buda-baki ranar Lahadi.