Daily Trust Aminiya - Tinubu ya bukaci ’yan Najeriya su rungumi zaman lafiya
Subscribe

Bola Ahmed Tinubu

Tinubu ya bukaci ’yan Najeriya su rungumi zaman lafiya

Jagoran Jam’iyyar APC na kasa, Asiwaju Bola Tinubu, ya bukaci al’ummar Najeriya da su rungumi zaman lafiya su manta da bambance-bambancen harshe da kabila da addini. 

Tinubu ya yi kiran ne a ranar Juma’a yayin addu’ar kwana bakwai da rasuwar gwamnan farko na farar hula a Jihar Legas, marigayi Alhaji Lateef Jakande.

Ya ce, Najeriya na fuskantar rikice-rikice amma duk da haka akwai bukatar ci gaba da zama a matsayin al’umma daya dunkulalliya mai cike da zaman lafiya.

“Yanzu Najeriya na fuskantar rikice-rikice da kalubalen tsaro ta kowace fuska da suka hada da garkuwa da mutane amma duk da haka Allah Ya sanya kasar a matsayin kasa guda kuma mafi girma da buwaya a cikin kasashe.

“Idan har akwai fadace-fadace, to ina zamu je? Za mu yi wa baki da ’yan kasashen Yammacin Afirka zagon kasa ne, kuma ba mu da wadataccen wurin da zai dauke mu bakidaya.

“Muna rokon Allah da Ya karfafi zuciyoyinmu, Ya yi mana jagora a imaninmu, Ya ba mu zaman lafiya a kasarmu, Ya albarkace mu bakidaya,” inji Tinubu.

Ya kuma bukaci malamai su dage da wayar da kan al’umma kan mawuyacin halin da ake ciki tare da gabatar da addu’o’i da azumi da kiraye-kirayen kan tabbatuwar zaman lafiya a Najeriya.

Tinubu, ya bayyana rasuwar Layeef Jakande a matsayin babban rashi ba ga iyalansa da Jihar Legas kadai ba, har ma ga al’umma bakidaya.

Ya ce Legas da Najeriya sun yi nasarar samun nagartaccen mutum kamar marigayin, duba da matsayinsa da kuma tarin iliminsa.

“Yau ba ma tare da shi amma har yanzu muna tare da irin kyawawan halayensa da ayyukansa da ya bari lokacin rayuwarsa.

“Muna wa Jihar Legas da Najeriya addu’r Allah Ya kara mana jama’a da nagartattun shugabanni masu gaskiya da amana da za su daga kimar kasar yanzu da ma nan gaba.”

More Stories