✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Sakamakwon Zaben Gwamnonin Najeriya Na 2023 (Alkaluma Daga:INEC)

Tinubu ya ci zabe a Jigawa

Jam'iyyar APC mai mulkin Najeriya ta yi nasara a zaben shugaban kasa a Jihar Jigawa.

Jam’iyyar APC mai mulkin Najeriya ta yi nasara a zaben shugaban kasa a Jihar Jigawa.

Baturen Zabe na Hukumar Zabe ta Kasa (INEC), Farfesa Armayau Hamisu na Jami’ar Tarayya da ke Dutsinma ya ce dan takarar shagaban kasa na APC ne ya zo a matsayi na da.

Wanda ya zo na biyu shi ne tsohon Mataimakin Shugaban Kasa, Atiku Abubakar sai kuma dan takarar NNPP, Sanata Rabiu Musa Kwankwaso, tsohon Gwamnan Jihar Kano na Jam’iyyar NNPP a matsayi na uku.

Ya bayyana cewa APC ta samu kuri’u 421,390, LP 1,889, NNPP 98,234 sai PDP 386,587.