✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Tinubu ya gana da Gwamnonin Arewa kan batun daukar Mataimaki

Ana dai harsashen zai dauki Mataimaki daga cikinsu

Dan takarar Shugaban Kasa na jam’iyyar APC, Asiwaju Bola Ahmed Tinubu, a ranar Alhamis ya gana da Gwamnonin jam’iyyar daga Arewacin Najeriya su 11 a Abuja, don tattauna batun wanda zai dauka a matsayin mataimakinsa.

Ganawar na zuwa ne a daidai lokacin da dan takarar ke ta kokarin daukar wanda zai dafa masa a takarar da zai yi a zaben 2023 mai zuwa.

Kasancewarsa wanda ya fito daga Kudancin Najeriya, ana sa ran dai Tinubu zai dauki Mataimaki ne daga Arewacin Najeriya.

Gwamnonin Arewa na jam’iyyar APC sun taka muhimmiyar rawa wajen samun nasarar Tinubu a takarar, musamman yadda suka tsaya kai da fata sai kujerar takarar ta koma Kudancin Najeriya.

A ranar Laraba ce dai kakakin Kungiyar Yakin Neman Zaben Tinubu, Bayo Onanuga, ya shaida wa gidan talabijin na Trust TV cewa an ware kujerar takarar Mataimakin ga Gwamnoni.

Tuni dai Hukumar Zabe ta Kasa Mai Zaman Kanta (INEC) ta ba jam’iyyu wa’adin mako daya su mika sunayen wadanda za su yi musu Mataimaka a takarar tasu.