✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Tinubu ya gana da kwamitin rikon APC

Kwamitin riko na jam’iyyar APC ya yi ganawar sirri da Uban Jam’iyyar Bola Tinubu, da nufin lalubo mafita daga rikicin da ya dabaibaye jam’iyyar. Gwamnan…

Kwamitin riko na jam’iyyar APC ya yi ganawar sirri da Uban Jam’iyyar Bola Tinubu, da nufin lalubo mafita daga rikicin da ya dabaibaye jam’iyyar.

Gwamnan Jihar Yobe, Mai Mala Buni da ‘yan kwamitinsa sun je gidan Tinubu ne a daren Alhamis, ‘yan awanni bayan ganawarsu da wani jigon jam’iyyar, Cif Bisi Akande domin neman shawarwarin sasanta bangarorin jam’iyyar.

Mai Mala Buni ya ce zamansu da Bisi Akande ya “ba wa kwamitin kwarin gwiwar samun nasara da goyon bayan dukkan iyayen jam’iyyar wajen sake karfafa ta”.

Kwamitin Zartarwar Jam’iyyar APC ya kafa kwamitin rikon ne domin sasanta bangarori da kuma shirya babban taro da zaben sabbin shugabanni bayan rikicin shugabancin da ya barke bayan kotu ta dakatar da Adams Oshiomhole, shugaban jam’iyyar na kasa.

Duk da cewa gwamnan bai fayyace abin da suka tattauna ba, rahotanni sun ambato Bisi Akande na cewa ya yi amannar kwamitin zai tsamo jam’iyyar daga rikicin ya kuma farfado da karsashinta.

“Kofata a bude take kuma ina kara kira ga dukkan masu ruwa da tsaki da su ba wa kwamitin hadin kai domin a yi nasara”, inji shi.

Sauran ‘yan kwamitin su ne gwamna Gboyega Oyetola na jihar Osun, Atiku Bagudu na jihar Kebbi da kuma Abubakar Sani Bello na jihar Neja.