Tinubu ya je Kano domin ta’aziyyar rasuwar kanin Dangote | Aminiya

Tinubu ya je Kano domin ta’aziyyar rasuwar kanin Dangote

    Clement A. Oloyede, Kano da Sagir Kano Saleh

Gwamnan Kano, Abdullahi Ganduje, ya jagaronci manyan ’yan siyasar jihar wurin tarbar Jagoran Jam’iyyar APC na Kasa, Bola Tinubu.

Tinubu ya je Kano ranar Juma’a ce domin ta’aziyya ga attajirin Afirka, Alhaji Aliko Dangote, kan rasuwar kaninsa, Sani.

Mamacin, Alhaji Sani Dangote, shi ne Mataimakin Shugaban Rukunin Kamfanin Dangote.

Ya rasu ne a ranar Lahadi a kasar Amurka inda ake jinyar shi, kafin a sallace shi ranar Laraba bayan an dawo da gawarsa.