✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Tinubu ya yi karar masu neman a soke zabe a kotu

Tinubu da APC sun ce masu neman a soke zaben ’yan hana ruwa gudu ne.

Dan takarar Shugaban Kasa na jam’iyyar APC, Asiwaju Bola Tinubu, ya kalubalanci masu adawa da zaben da aka gudanar ranar Asabar a gaban Kotu.

Aminiya ta ruwaito cewa, manyan jam’iyyun adawa da suka hada da PDP da LP sun bukaci a soke Babban Zaben da aka gudanar tare da neman a gudanar da sabo.

Sai dai a karar da Tinubun da jam’iyyar APC suka gabatar a gaban wata Babbar Kotun Tarayya da ke zamanta a Jihar Kano, sun nemi a hana jam’iyyun aiwatar da kowane irin yunkuri na dakatar da ci gaba da tattarawa da bayyana sakamakon zaben da aka gudanar a karshen mako.

A kunshin karar mai lamba FHC/KN/CS/43/2023 da aka gabatar a gaban kotun a wannan Talatar, Hukumar Zabe ta Kasa INEC na cikin wadanda ake tuhuma yayin da dan takarar Mataimakin Shugaban Kasa na APCn, Kashim Shettima ke rukunin masu gabatar da kara.

Wakilinmu ya ruwaito cewa, jam’iyyar APC na neman kotun ta yi wa duk wadanda take karar shamaki na hana ci gaba da tattarawa da bayyana sakamakon zaben.