✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

‘Tinubu ya yi wa Gwamnonin APC alkawarin Mataimakin Shugaban Kasa’

Tinubu dai ya yi wa Gwamnonin alkawarin daukar daya daga cikinsu

Dan takarar Shugaban Kasa na Jam’iyyar APC, Bola Tinubu, ya ce ya yi wa Gwamnonin jam’iyyar alkawarin daukar daya daga cikinsu don ya yi masa Mataimaki a zaben 2023.

Kakakin Kungiyar Yakin Neman Zabe na Tinubu, Bayo Onanuga, shi ne ya bayyana hakan cikin wani shiri da gidan talabijin na Trust TV a ranar Laraba.

Ya ce, a lokacin da ya gana da Kungiyar Gwamnonin APC,  Tinubu ya dau musu alkawarin zabo wanda zai yi masa Mataimaki daga cikinsu.

“Sa’ilin da Tinubu ya gana da Gwamnonin, ya fada musu cewa, ku ne za ku zabi wanda za mu yi takara tare da shi,” inji Onanuga.

Ya ci gaba da cewa, bincike ya nuna matsalar Najeriya ba ta addini ba ce, face rashin tsaro da tattalin arziki da rashin aiki da sauransu, wanda su ne sama da kashi 70 na bukatun ‘yan kasa.

Daga nan ya ce, batun addini a cikin sha’anin siyasa ba shi ne matsalar ’yan Najeriya ba.

Ya ba da misalin yadda a 1993, yadda MKO Abiola da Babagana Kingibe suka lashe zabe alhali su biyun Musulmai ne.

Game da yadda Tinubu zai jawo sauran ’yan takarar da suka sha kaye don a hadu a yaki PDP, Onanuga ya ce Tinubu mutum ne mai zuciyar yafiya, har ma da wadanda suka munafurce shi.

Don haka, ya ce Tinubu ya sha alwashin tafiya da kowa don samun nasarar jam’iyyarsu a 2023.

Bola Tinubu ya samu tikitin takarar Shugaban Kasa ne bayan da ya lashen zaben fid-da gwanin da APC ta gudanar, inda ya samu kuri’a 1,271 daga cikin baki dayan kuri’un da aka jefa.