✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Tinubu ya ziyarci Buhari a Fadar Aso Rock

Tsohon gwamnan na Jihar Legas ya shiga bayan labule da Shugaba Buhari.

Jigo a jam’iyya mai mulki ta APC, Asiwaju Bola Ahmed Tinubu, ya kai wa Shugaban Kasa Muhammadu Buhari ziyara a Fadar Gwamnatin Kasar ta Aso Rock da ke Abuja.

Wakilinmu ya ruwaito cewa, a halin yanzu tsohon gwamnan na Jihar Legas ya shiga bayan labule da Shugaban Kasar inda suke kus-kus kan wani lamari da har kawo yanzu ba samu wani haske a kansa ba.

Sai dai ana kunji-kunjin cewa ganawar ba za ta rasa nasaba da jan kafar da ake yi ba wajen tsayar da ranar da za a gudanar da babban taron jam’iyyar APC, wanda a nan ne za ta zabi shugabanninta.

Tuni dai ta bayyana cewa Tinubu na daga cikin jiga-jigan jam’iyyar APC da ke hankoron samun tikitin takarar kujerar shugaban kasa a zaben 2023 da ke tafe.

A Juma’ar da ta gabata ce Shugaban Kungiyar Gwamnonin Arewa, Gwamna Simon Bako Lalong na Jihar Filato, ya ganawa da Shugaba Buhari a kan batun babban taron jam’iyyar.

Jim kadan bayan ganawar ta su ce kuma Shugaban Kwamitin Riko na jam’iyyar APC na kasa, Gwamna Mai Mlaa Buni na Jihar Yobe, shi me ya gana da shugaban kasar kan babban taron wanda shi jam’iyyar ta sanya gaba a halin yanzu.

Kazalika, a wata hira ta musamman da ya yi da Gidan Talabijin na Kasa NTA, Shugaba Buhari ya gargadi jam’iyyar a kan ta yi taka tsan-tsan wajen warware duk wasu matsalolinta don gudun kada wata jam’iyyar adawa ta yi mata mahangurbar kwace madafan iko a zaben 2023.

Da dama dai daga cikin ’ya’yan jam’iyyar ta APC na ci gaba da bayyana damuwa kan makomar jam’iyyar, inda ake ta yi wa shugabanninta matsin lamba dangane da jan kafar da ake yi na fara shirye-shiryen babban taronta da ake sa ran gudanar da shi a watan Fabrairu.