✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Tinubu ya ziyarci Sarkin Kano, zai gana da sarakuna

Gwanma Ganduje ya yi masa rakiya zuwa Fadar Sarkin Kano

Jagoran Jam’iyyar APC na Kasa, Asiwaju Bola Ahmed Tinubu ya ziyarci Sarkin Kano, Alhaji Aminu Ado Bayero.

Tinubu wanda Gwamna Kano Abdullahi Ganduje ya raka zuwa fadar sarkin, zai gana da Sarakunan Arewacin Najeriya a ranar Litinin.

A yayin ziyarsa Kanon ne kuma tsohon Gwamnan Jihar Legas din zai gudanar da bikin cikarsa shekara 69 a a duniya.

Da yake jawabi a Fadar Sarkin Kano, Tinubu ya ce Najeriya na cikin wani yanayi da mafita ita ce hadin kan al’umma domin kawo wa kasar cigaba da nasarori.

“Najeria na cikin tsaka mai wuya kuma abin da take bukata domin dorewarta su ne hadin kai da fahimtar juna, saboda haka wajibi ne jihohin Legas da Kano da suka jima suna fama da wadannan matsaloli, su ne za su nemo mafita.

“Za a rasa zaman lafiya da cigaba muddin aka bari abubuwa suka ci gaba da gudana kamar yadda suke a halin yanzu; Dole ne a yi fatan samun zaman lafiya da hadin kai ga kasar,” inji shi.

“Yanzu ga ni, Bola Tinubu, zaune a gefen Gwamna Ganduje, wanda haka alama ce a fili cewa mutane, komai addini ko kabilarsu, za su iya hada kai a domin samar da canji,” inji Tinubu.

Ya ce jihohi kamar Kano da Legas na da gagarumar rawar takawa wajen jagorancin hadin kasa saboda yanayinsu na tara al’ummomi iri-iri.

A jawabinsa, Sarkin Kano, Aminu Ado Bayero, ya yaba masa da ya zabi Kano don bikin cikarsa shekaru 69 da haihuwa, wanda ya ce shaida ce ta kaunarsa ga samun hadin kai a Najeriya.

Sau biyu ke nan Tinubu na ziyartar Jihar, inda a ziyarsa a watan Disambar 2020 ya gana da wasu malamai magoya bayan burinsa na zama shugaban kasa a 2023.

A cikin ’yan kwanakin nan, tsohon gwamnan na Jihar Legas ya ziyarci jihohin Kaduna, Kano da Katsina wadanda suka fi yawan masu jefa kuri’a a Najeriya.