✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto

Tirela ta kashe mutum 5 a Kogi

Hatsarin ya auku ne sakamakon kwacewar da babbar motar ta yi ta haye kan karamar motar.

Mutum biyar aka rawaito sun mutu, sannan hudu suka jikkata sakamakon mummunan hatsarin mota da ya rutsa da su a yankin Okene na Jihar Kogi.

Hatsarin wanda ya auku ranar Litinin da misalin karfe 7:00 na dare, ya shafi  wata tirela da kuma karama mota.

Hatsarin ya auku ne sakamakon kwacewar da babbar motar ta yi ta haye kan karamar motar.

Hukumar Kiyaye Hadurra ta Kasa (FRSC), ta tabbatar da faruwar hakan, tare da cewa hatsarin ya auku ne a mararrabar Oro da ke yankin.

Majiyarmu ta ce, lamarin zai iya fin haka muni ba don karamar motar ta yi wa babbar burki ba.

Kwamandan FRSC a yankin, Steve Dawulong ya ce,  “An dauki gawarwakin wadanda suka mutu zuwa Babban Asibitin Okengwe, sannan wadanda suka jikkata ’yan uwansu sun kwashe su.”