✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Tirela ta murkushe sojoji 2, ta jikkata daya a Kwara

Tirelar ta bi ta kan dakarun sojin lokacin da suke bakin aiki.

Wasu dakarun Sojin Sama sun rasu, wani daya ya samu mummunan rauni sakamakon kwacewar da wata tirela ta yi ta bi ta kansu a Jihar Kwara.

Lamarin da ya faru a daidai gadar Pasa a yankin Eyenkorin daf da Barikin Sojin Sama, ya haifar da rudani a tsakanin sojoji da mazauna yankin.

Sakataren Kwatin Zartarwa na Jihar Kwara, Shola Musa, ya ce lamarin ya faru sakamakon tsinkewar birkin tirelar.

“Na kira rundunar ’yan sanda su je wajen da lamarin ya faru don tabbatar da doka da oda sakamakon rudani da aka shiga a yankin,” kamar yadda ya bayyana wa Aminiya.

A lokacin da wakilanmu ya ziyarci yankin a ranar Talata, ya iske motar sojin sama mai lamba AF 496 CO1 girke a wajen da lamarin ya faru tana jiran ko ta kwana.

A cewar wani ganau, da ya ce sunansa Alhaji Pasa, “Dakarun suna cikin aiki lokacin da burkin tirelar ya tsinke ya murkushe biyu daga cikinsu ta ji wa daya mummanan rauni a shingen bincikensu.

“Direban tirelar ya yi kokarin tserewa bayan faruwar lamarin amma sojojin da ke wajen sun harbe shi a kafa. Mutanen yankin sun bukaci tun farko a cire shingen bincike a wajen amma ba a cire ba,” a cewarsa.

Kakakin Hukumar Kiyaye Haddura ta Kasa (FRSC) na Jihar Kwara, Okasanmi Ajayi, ya ce, “Na samu labari, amma ba ni da cikakken bayani game da abin da ya faru, watakila an kwashe wadanda abun ya rutsa da su kafin mutanenmu su je wajen.”

Shi kuwa kakakin Rundunar Sojin Sama da ke Ilorin, Mathew Adeniyi, da aka tuntube shi cewa ya yi “wane ne ya ba ka wannan bayanin?

“Yanzu haka ina hutu, sai na je hedikwata sannan zan bincika abin da ya faru,” in ji Adeniyi.