✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Tirela ta muttsike mutane da dabbobi a Kwara

Tirelar da ta fito daga Arewacin Najeriya dauke da shanu ta auka kan wata mota da ke tsaye a gefen titi.

Mutum takwas tare da dabbobi da ba a iya tantance yawansu ba sun rasu bayan wata tirela makare da shanu ta bi ta kansu a Jihar Kwara.

Wannan al’amari ya faru ne bayan tirelar da ta fito daga Arewacin Najeriya dauke da shanu ta auka kan wata mota da ke tsaye a gefen titi.

Kwamandan Hukumar Kiyaye Haddura ta Kasa (FRSC) a Jihar Kwara, Frederick Ogidan ya ce “Hatsarin ya ritsa da mutum 17 ne; takwas sun rasu wasu hudu kuma sun samu rauni.”

Wani shaida ya ce “Cikin mamatan har da masu sayar da dabbobi da sauran ’yan tireda da ke wurin; abin ya yi muni sosai.”

Ya bayyana cewa ana kyautata zaton wani mutum da ya rasu nan take a cikin motar shanun shi ne mai su.

Ya ce hatsarin ya auku ne a Mahadar Okoolowo, da ke Karamar Hukumar Ilorin ta Kudu a ranar Laraba da misalin karfe 6 na safe.

Wani ganau ya ce mutum 12 ne suka samu rauni, kuma an kai gawarwakin dakin ajiyar gawa na Babban Asibitin Ilorin.