✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Tirela ta take amarya ana dab da bikinta

‘Yan uwa da abokan arzikin wata amarya da ake dab da bikinta sun kasance ciki alhini bayan wata babbar mota ta hallaka ta. Amaryar mai…

‘Yan uwa da abokan arzikin wata amarya da ake dab da bikinta sun kasance ciki alhini bayan wata babbar mota ta hallaka ta.

Amaryar mai suna Immaculate Okochu ta gamu da ajalinta ne bayan da ta hau babur na acaba a lokacin da take kan hanyarta na zuwa wajen aiki,  inda wata tirela ta yi kanta ta kuma take ta a yankin Ajah a Legas.

An garzaya da Immaculate asibiti inda ta ce ga garinku.

Kawar marigayiyar, Lucy Ibe, wacce ita ke jagorantar tsare-tsaren bikin amaryar da ake shirin yi, ta shaida wa Sashen Turancin Fijin na BBC cewa amaryar ta rasu ne a ranar Laraba 12 ga watan Agusta, ranar da babbar motar ta take ta.
“Ba nan take ta mutu ba, da fari an kai ta wani asibiti a yankin da lamarin ya auku, daga nan kuma aka kai ta Babban Asibitin Gwamnati da ke Marina a cikin garin Legas.
“A lokacin da na je asibitin na iske ta a bayan motar da aka kai ta asibitin ana ba ta agajin gaggawa, an sanya mata ruwa, ba a kai ga karbar ta a cikin asibitin ba ta mutu.
‘Yan uwa da abokan arzikin amaryar sun yi ta sanya hotonta a kafafen sada zumunta domin nuna alhini da kuma mika ta’aziyya.