✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Toshe Twitter ya jawo wa Najeriya asarar N247.61bn

A kwana 100 da aka toshe Twitter Najeriya ta yi asarar makudan kudade.

Toshe kafar sa da zumunta ta Twitter da Gwamnatin Najeriya ta yi ya cika kwana 100, tare da ja wa kasar asarar Naira biliyan 247.6.

A ranar 4 ga watan Yuni, 2021 ne Gwamnatin Tarayya ta ba da umarnin dakatar da Twitter a Najeriya, bayan goge wani rubutu da Shugaban Kasa Muhammadu Buhari ya yi kan ’yan a-waren Biyafra.

A sakamakon haka, a ranar 5 ga watan Yuni kamfanonin sadarwa suka toshe hanyar shiga shafin Twitter bayan sun samu umurni yin hakan daga Hukumar Sadarwa ta Kasa (NCC).

Cibiyar NetBlocks Cost of Shutdown Tool, da ke kiyasta adadin shige da ficen kudade ta kafar Intanet, ta ce toshe Twitter ya kawo wa tattalin arzikin Najeriya koma baya inda take asarar miliyan N103.17 a kowace awa.

Sai dai Fadar Shugaban Kasa ta hannun Ministan Yada Labarai da  Raya Al’adu, Lai Mohammed, ta ce tana dab da cim ma yarjejeniya da Twitter tare da janye takunkumin da ta dora mata.

Najeriya ta shiga cikin sahun kasashen da aka hana amfani da Twitter wadanda suka hadar da kasashe kamar China, Iran, da Koriya ta Arewa.

Wani kamfani, ExpressVPN ya ce ya samu karuwar sama da kashi 200 cikin dari na masu amfani da intanet daga Najeriya tun daga lokacin da gwamnatin kasar ta toshe Twitter.