✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto

Tottenham ta kulla yarjejeniyar daukar Ivan Perisic daga Inter Milan

Perisic ya rattaba hannu kan kwantaragin kakar wasanni biyu a Tottenham.

Kungiyar kwallon kafa ta Tottenham Hotspur ta kammala kulla yarjejeniyar daukar dan wasan gaban Inter Milan, Ivan Perisic.

Tottenham ta dauki Perisic mai shekara 33 kyauta bayan kwantaraginsa ya kare a Inter Milan, kungiyar da ta kare a mataki na biyu a gasar Serie A ta bana a Italiya.

Perisic dan kasar Croatia ya rattaba hannu kan kwantaragin kakar wasanni biyu a kungiyar da ke buga Firimiyar Ingila, bayan an kammala gwaje-gwajen tabbatar da ingancin lafiyarsa.

A ranar 30 ga watan Yuni Perisic zai koma kungiyar ta Arewacin Landan a hukumance bayan karewar kwantiraginsa a San Siro.

Perisic ya lashe gasar Serie A a kakar wasanni ta 2020-21.

Ya kasance daya daga cikin manyan ’yan wasan Inter Milan a kakar 2021-22, inda ya zira kwallaye takwas tare da taimaka wa kwallaye bakwai a wasanni 35 da ya buga a gasar Serie A ta bana wadda suka kare a mataki na biyu.