✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Trump na kwadayin sake shugabancin Amurka

Idan har Mista Trump ya ci zaben 2024, shi da Shugaba Biden za su yi hannun karba, hannun mayarwa

Tsohon Shugaban Amurka da aka kayar a zaben 2020, Donald Trump, yana son sake tsayawa takara a zaben 2024.

Ya bayyana hakan ne shekara guda bayan Sanata Joe Biden ya kayar da shi a yayin da yake neman tazarce a Fadar White House.

Idan har Mista Trump ya lashe zaben Amurka na 2024, ‘hannun karba, hannun mayarwa’ za a yi a Fadar White House tsakaninsa da Shugaban Joe Biden mai ci.

A wata hira da jaridar The Guardian ta  yi da Trump, ta tambaye shi dalilinsa na neman komawa fadar White House, duk da tankiyar da gwamnatinsa ta yi ta samu da bangaren Majalisa har ta nemi tsige shi, gami da bincike kan zargin alakar gwamnatinsa da kasar Rasha.

Budar bakinsa ke da wuya, sai ya ce, “Ina kaunar kasarmu. Na kuma kawo mata daukaka da ba ta taba samun irinsa ba.”

Ya kuma yaba wa gwamnatinsa kan abin da ya kira “ceto rayuwar miliyon mutane da fadin duniya” ta hanyar samar da rigakafin cutar COVID-19; Duk da cewa ana zargin gwamnatin tasa da yi wa bullar cutar a kasar rikon sakainar kashi.

Sauran abubuwan da aka tattauna da shi sun hada da tarzomar da magoya bayansa suka kutsa cikin ginin Majalisar Amurka domin hana ta tabbatar da nasarar Sanata Biden a kansa a zaben ranar 3 ga watan Nuwamban 2020.

Sauran sun hada da zanga-zanga kan kashe bakaken fata a kasar, rikicin kan iyakan Amurka da Meziko, ficewar kasar Birtaniya daga Tarayyar Turai da kuma kungiyoyin kare hakki da dai sauransu.