✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Trump ya maka Twitter a kotu kan kin bude shafinsa

Trump ya ce hakan zai bashi damar ci gaba da amfani da shafin kamar kowa.

Tsohon Shugaban Amurka, Donald Trump, a ranar Juma’a  ya bukaci kotu da ta tursasa kamfanin sada zumunta na Twitter ya bude masa shafinsa.

Trump ya ce hakan zai bashi damar ci gaba da amfani da shafin kamar kowa.

Tsohon Shugaban ya mika koken ne gaban wata kotun Amurka da ke gundumar Kudancin Florida, inda ya ce ’yan Majalissar Dokokin kasar ne suka tursasa kamfanin na Twitter suka rufe masa shafin nasa kamar yadda Kamfanin Dillancin Labarai na Reuters ta rawaito.

Sai dai da Reuters ya tuntubi kamfanin na Twitter, ya ki cewa uffan kan shigar da karar.

Kafin a rufe shafin nasa, Trump yana da mabiya sama da miliyan 88 a dandalin.

A watan Janairun 2021 ne dai kamfanin ya rufe shafin Trump saboda zargin yin amfani da shi wajen tunzura jama’a da kuma yada labaran karya.