✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Trump ya umarci a janye dakarun Amurka daga Somaliya

Donald Trump ya umarci a janye dakarun kasar sa daga Somalia

Ma’aikatar Tsaron Amurka ta Pentagon ta ce Shugaba Donald Trump ya umarci a janye dakarun kasar sa daga Somaliya daga ranar 15 ga watan Janairun 2020.

Kasar dai na da dakaru kusan 700 a Somaliya wadanda suke taimaka wa sojojin kasar wajen yaki da kungiyar Al-Shabab.

A ‘yan watannin nan dai shugaba Trump ya ba da makamancin wannan umarnin na rage yawan dakarun kasar sa a Iraki da Afghanistan.

Ya ce kamata ya yi sojojin su dawo gida, yana mai cewa tsarin tafiyar da sojojin a kasashen waje na da matukar tsada kuma kwalliya ba ta biyan kudin sabulu.

Aiwatar da umarnin dai zai zo ne ‘yan kwanaki kadan kafin Trump ya bar karagar mulkin Amurkan, ko da dai ya ce hakan ba yana nuna yin mi’ara koma baya ga manufofin Amurka a kasashen waje ba ne.

Sanarwar ta Pentagon ta ce, “Za mu ci gaba da yaki da dukkan wasu kungiyoyi masu tsattsauran ra’ayi da za su iya barazana ga wanzuwar kasar mu.”

Kasar Somaliya dai ta jima tana fama da rikice-rikicen siyasa, ko da dai a ‘yan shekarun nan Amurka ta taimaka mata wajen kwato birnin Mogadishu da ma wasu yankunan daga Al-Shabab.