Daily Trust Aminiya - Trump ya yi barazanar barin Amurka matukar ya fadi zaben shu
Subscribe

Shugaban Amurka Donald Trump

Trump ya yi barazanar barin Amurka matukar ya fadi zaben shugaban kasa

A wani mataki mai cike da almara, shugaban Amurka Donald Trump ya yi harsashen abinda zai iya faruwa idan ya fadi zaben kasar dake tafe.

A watan Nuwamba mai zuwa ne dai za a fafata tsakanin shugaban dake neman wa’adi na biyu karkashin jam’iyyar Republican da kuma abokin karawarsa na Democrat, Joe Biden.

Kalaman na Trump dai na zuwa ne lokacin da yake jawabi yayin gangamin yakin neman zabensa a jihar Georgia a daren ranar Juma’a.

Trump ya ce, “Kun san me? Yin takara da wanda ya fi kowa tabarbarewa a tarihin ‘yan takarar shugabancin kasa a tarihin Amurka ya hana ni samun natsuwa.

“Me ku ke tunani zai faru in na fadi a wannan zaben? Tirkashi! Me ma zan yi kuma a ina zan saka kaina? Cewa na fafata da mafi tabarbarewar dan takara kuma ya kayar da ni!

“Gaskiya ba zan ji dadi ba, watakila kawai barin kasar zan yi. Ban ma san me zan yi ba,” inji shugaba Trump.

A mafi yawan kuri’un jin ra’ayin jama’ar da aka gudanar a Amurka dai na nuna shugaban na kan gaban Joe Biden.

Sai dai Trump zai iya fuskantar tuhume-tuhume iri-iri in bai kai bantensa ba a zaben na watan Nuwamba.

More Stories