✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Tsadar rayuwa ta kai matakin intaha a Jamus

Jamus ta fuskanci tashin farashin da ya kai maki 7.9 cikin 100.

Tsadar kayayyaki a Jamus ta kai kololuwar da ba a taba gani a kasar ba tun bayan hadewar Yammaci da Gabashin kasar.

Kafar Watsa Labarai ta DW ta ruwaito cewa a watan Mayu abin ya fi muni bayan tashin farashi mai radadi da kasar ta shaida a Afrilun bana.

Hukumar Kididdigar Kasar ta sanar da haka a cikin rahotonta na wannan wata na Mayu mai karewa, inda ta ce Jamus ta fuskanci tashin farashin da ya kai maki 7.9 cikin 100.

Hukumar ta alakanta tsadar rayuwar da ake fuskanta a Jamus din da rikicin Ukraine wanda ya haddasa tsadar farashin makamashin gas da fetur.

Tun da farko hukumomin kasar sun ce suna tunkarar wannan kalubale ta hanyar rage farashin tikitin jirgin kasa na watanni uku da bayar da tallafi ga man fetur a fadin kasar.