✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Tsagin Shekarau ya yi fatali da sulhun uwar jam’iyya kan rikicin APC a Kano

Ta yaya mutane biyu su na jayayya, sai kuma a ce daya daga cikinsu shi ne zai jagoranci sasanci a tsakaninsu.

Tsagin da tsohon gwamnan Jihar Kano, Sanata Ibrahim Shekarau ke jagoranta ya yi watsi da sulhun da  uwar jam’iyyar APC ta yi kan rikicin da mamaye reshenta na Jihar Kano.

Wannan ya nuna cewa rikicin shugabancin jam’iyyar APC a Kano na kara daukar sabon salo bayan da tsagin na Shekarau ya yi fatali da sanarwar uwar jamiyyar na bai wa Gwamna Abdullahi Umar Ganduje jagorancin kwamitin da zai warware matsalar da ke tsakanin bangarorin biyu.

A wata hirarsa da manema labarai  jim kadan bayan fitowar sanarwar jam’iyyar APC ta kasa, Sanata Ibrahim Shekarau ya ce sun yi watsi da wannan sanarwa kuma ba su amince da ita ba.

“Matsayinmu akan wannan sanarwa matakai ne kamar guda uku: a duk zaman da muka yi kamar sau biyu ko sau uku, wanda mai girma gwamna Ganduje ya na wurin da mukarrabansa da wadanda mu ma muka je tare da su, karkashin jagorancin shugaban jam’iyyar gwamnan jihar Yobe Maimala Buni.

“An nemi kowanne bangare ya bayyana matsayarsa da abin da suke son a yi da shawarar warware wannan matsala, duk mun bayar da na mu. Shugaban jam’iyya ya ce za su koma su kalli bayanan da duk muka yi domin fito da wata matsaya, da shawarar abin da ya dace a yi.”

Sanata Shekarau ya kara da cewa, “sanarwar da jam’iyyar APC ta fitar ba ta yi magana a kan matsayar da aka cimma tsakanin bangarorin biyu ba, sannan jam’iyya ba ta fadi komai tsakanin abin da bangarorin biyu suka bukata ba.

“Abu na biyu kafin a kawo takardar a matsayin wanda ya ke jagorantar daya bangaren, sai da aka kai wa gwamna Ganduje takardar wadda kamata ya yi ta zama tsakanin shugaban jam’iyyar, ko hedikwatar jam’iyya, da gwamna da kuma ni shugaban dayan barin jam’iyyar,” in ji Shekarau

Sannan ya ci gaba da cewa kafin su samu takardar sai da ta shiga duniya tana yawo a shafukan sada zumunta.

“Yaran gwamna na cewa an dankawa gwamna jam’iyya ai ta koma hannunsa da maganganu makamantan haka.

“Abu na uku shi ne yaya mutane biyu su na jayayya, sai kuma a ce daya daga cikin wadanda ake jayayya da shi ne zai jagoranci sasantawar, alhalin shi ya jagoranci waccan sasantawar da ba a yi mana adalci ba, da muke ganin an zalunce mu, ta ya ya za a yi mana adalci a yanzu.

“Kamata ya yi uwar jam’iyya ta wakilta wanda zai jagoranci wannan zama. Don haka ba mu amince da shi ba, mun yi fatali da shi, ba mu yarda ba, ba kuma za mu amince ba, a karshen takardarmu mun fadawa uwar jam’iyya mu masu biyayya ne, a shirye muke a sake zama domin sasantawa,” in ji Shekarau.

Shekarau ya ce wannan dalili ya sa suka rubuta takarda suka aika wa shugaban jam’iyya, za kuma su bai wa ’yan jarida da shafukan sada zumunta cewa abin da sukayi tsammani a yi ba shi aka yi ba.

Da yake ganawa da Aminiya ta wayar tarho a ranar Lahadi, mai magana da yawun tsagin Shekarau, Dokta Sule Yau Sule, ya ce a zaman sulhun da aka yi a ranar Asabar, an fitar da yadda za a yi raba daidai na shugabancin jam’iyyar a tsakanin bangarorin biyu.

Shi ma a nasa bangaren, Kwamishinan Labaran Jihar Kano, Muhammad Garba, ya ce muhimmanci sulhu a jam’iyyar APC reshen Jihar Kano ya sanya kowane bangare yake hankoron ganin an samu zaman lafiya da kwanciyar hankali a jam’iyyar.

Abin da sanarwar uwar jam’iyyar ta kunsa

A daren Litinin ne uwar jam’iyyar ta fitar da sanarwa kan yadda za a shawo kan matsalarsu da magance ta.

Ta kafa kwamitin mutum biyar domin warware rikicin shugabanci da ya ki ci ya ki cinyewa a Jihar Kano tsakanin bangaren Sanata Ibrahim Shekarau da na gwamna Abdullahi Umar Ganduje.

Jam’iyyar ta sanya gwamna Ganduje a matsayin shugaban kwamitin, sai kuma Sanata malam Ibrahim Shekarau a matsayin mataimakinsa.

Dukkan mutanen biyu dai na ja-in-ja kan shugabancin jam’iyyar APC a jihar ta Kano, lamarin da ya janyo takun saka da sanya jam’iyyar cikin halin kaka-ni-kayi a jihar.

Sauran ’yan kwamitin akwai gwamnan Jihar Zamfara Bello Muhammad Matawalle, da tsohon Kakakin Majalisar wakilai Yakubu Dogara, da Sanata Abba Ali, da kuma wakilin jam’iyyar da ke sa ran za a yi zama da shi.

Sanarwar ta kuma ci gaba da cewa ana san kwamitin zai yi zama a Jihar Kano cikin kwanaki bakwai tare da mikawa jam’iyyar rahoto.

Sannan tana fatan bai wa gwamna Ganduje shugabancin kwamitin a matsayinsa na kamar shugaban jam’iyyar APC a Jihar Kano zai nuna kyakkyawan shugabanci a zaman da za a yi.

APC ta ce an dauki matakin ne saboda kotu ta gagara warware rikicin, alhalin dukkan bangarorin biyu ba za su kai labari ba a lokacin zabe dole sai da dan uwansa.

Sanarwar ta kara da cewa, domin samun warware matsalar da samun jam’iyya guda ba kungiya-kungiya a jihar ta Kano, ya na da matukar muhimmanci gwamna Ganduje ya jagoranci kwamitin.

Haka kuma, adalcin a nan ba wai rarraba madafun iko na jam’iyyar kadai ba ne, har da yi wa sauran ’yan jam’iyyar adalci ta fuskar shugabanci.