Tsagin Shekarau ya zabi Danzago a matsayin shugaban APC na Kano | Aminiya

Tsagin Shekarau ya zabi Danzago a matsayin shugaban APC na Kano

    Ishaq Isma’il Musa da Clement A. Oloyede

Tsagin tsohon Gwamnan Jihar Kano, Malam Ibrahim Shekarau, ya zabi Ahmadu Haruna Danzago a matsayin sabon shugaban jam’iyyar APC na jihar.

Bayanai sun ce tsagin ya gudanar da zaben ne a wani wuri a Unguwar Janguza da ke Karamar Hukumar Tofa ta jihar.

Hakan dai na zuwa ne bayan da tsagin Gwamna Abdullahi Umar Ganduje, ya zabi Abdullahi Abbas a matsayin shugaban jam’iyyar APC na jihar.

Ahmadu Haruna Danzago

Wannan lamari dai ya sake tabbatar da barakar da ta mamaye ’ya’yan jam’iyyar APC a Jihar Kano.