✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto

Tsananin sanyi ya hallaka mutum 52 a Amurka

Jami’an agaji na ci gaba da ciro gawarwakin mutanen da dusar kankara ta binne a yankin Buffalo

Jami’an agaji na ci gaba da ciro gawarwakin mutanen da dusar kankara ta binne a yankin Buffalo da ke binrin New York, bayan mutuwar mutane 28 ranar Litinin.

Rahotanni na nuna sauran yankunan Amurkan na cikin fargaba, sakamakon mummunar guguwar hunturu da dusar kankara da suka yi ajalin fiye da mutum 24 a sassan kasar gabanin mace-macen na yankin Buffalo.

Shugaban lardin, Mark Poloncarz, ya ce, “Wannan hunturu dai shi ne mafi muni a tarihi kuma akwai wadanda kwanansu biyu cikin mota sun rasa yadda za su fito, saboda tsananin sanyi da guguwar hunturun, da kuma tudun dusar kankara.”

Mark Poloncarz ya ce mutane da dama sun mutu a cikin motocinsu, wasu a gidajensu, wasu kuma lokacin da suke kokarin tone dusar kankara don samun hanya, musamman a yankin Buffalo.

Ya ce hukumar kula da yanayi ta kasar ta yi hasashen za a samu saukar akalla inci tara na dusar kankara ranar Talata, musamman a Arewacin New York.

Wani rahoto na BBC ya rawaito cewa tsananin sanyi da guguwar hunturu sun hallaka mutum 56 a yankunan da ke kan iyakokin kasashen Canada zuwa Mexico.