✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto

Tsarin IPPIS: Buhari ya dakatar da biyan albashin lakcarori

Dokta Nsikak Ben, shi ya sadar da sakon dakatar da biyan albashin cikin wata wasika.

Bisa umarnin Shugaban Kasa Muhammadu Buhari, Ofishin Babban Akanta na Najeriya, ya dakatar da biyan albashin dukkanin Lakcarorin da basa kan tsarin IPPIS, sabon tsarin biyan albashin ma’aikata na bai daya da Gwamnatin Tarayya ta kawo.

Daraktan gudanar da tsarin IPPIS na Ofishin Akanta na Kasa, Dokta Nsikak Ben, shi ya sadar da sakon dakatar da biyan albashin cikin wata wasika mai dauke da kwanan watan ranar 8 ga watan Oktoba wadda da aka aikewa dukkanin Shugabannin Jami’o’in Gwamnatin Tarayya da ke fadin kasar.

Wasikar wadda aka aika ta hanyar Kwamitin Shugabannin Jami’o’in Gwamnatin Tarayya, an kuma mika kwafinta ga kowane babban jami’in shige da ficen kudi na jami’o’in.

Wasikar ta ce: “An umarce ni na sanar da ku cewa dukkan wani ma’aikacin jami’a da bai shiga tsarin biyan albashi na IPPIS ba a sakamakon tafiya hutun karo karatu ko haihuwa ko rashin lafiya, sunansa ba zai taba bayyana a tsarin ba daga yanzu zuwa watan Nuwamban 2020.”

“Saboda haka kowani ma’aikaci ya gabatar da bayanansa domin Ofishin Babban Akantan Kasa ya shigar da shi cikin tsarin.”

“Doriya a kan wannan, wasiikar ta ce “dukkanin wasu bayanai da ake bukata a hada su tare da shaidar bayanan asusun ajiyar banki na albashin watanni shida na baya-baya.

“Yana da kyau ku sanar da ma’aikatanku wadanda wannan abun ya shafa da su hanzarta gabatar da kansu domin a shigar da bayanansu cikin tsarin.”

“Sai dai an ba da dama jami’o’i su gabatar da shaidar ma’aikatan da suka dauki hutun karo karatu, tare da bayyana tsawon lokacin da kowane ma’aikaci zai shafe gabanin kammala karatun.”