✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto

Tsaro: An haramta hawan babur na wasu lokuta a Katsina

Bayan bai wa masu satar shanu da garkuwa da mutane wa’adin kwanaki biyu da su mika wuya tare da sako wadanda suka yi garkuwar da…

Bayan bai wa masu satar shanu da garkuwa da mutane wa’adin kwanaki biyu da su mika wuya tare da sako wadanda suka yi garkuwar da su ba tare da wani sharadi ba.

Gwamnan jihar Katsina Aminu Bello Masari, a jiya Laraba ya rattaba hannu kan wata doka data hana hawan babura daga karfe 7 na dare zuwa 6 na safe a duk fadin Jihar sakamakon kalubalen tsaron da ake fuskanta.

Kamar yadda Kwamishinan Shari’a Ahmad Al-Marzuk, ya ce daukar wannan matakin ya zama dole domin dakile duk wata hanyar da ‘yan ta’addar zasu yi amfani ita.

Jami’an tsaro ne kawai dokar ta bai wa izinin hawan baburan, wato, sojoji, ‘yan sanda, Sibil difensi da sauran masu sanya kayan sarki.

“Duk wanda ya karya dokar za’a daure shi har na tsawon shekara daya a gidan maza ko kuma ayi masa tara ko hada duka biyu.” Ita dai wannan doka zata fara aiki daga ranar Litinin 20 ga watan Janairu 2020.