Tsaro: Faransa ta musanta juya baya ga Mali | Aminiya

Tsaro: Faransa ta musanta juya baya ga Mali

Emmanuel Macron, Shugaban Faransa a wurin jana’izar Idriss Deby. (Hoto: Christophe PETIT TESSON / POOL / AFP)
Emmanuel Macron, Shugaban Faransa a wurin jana’izar Idriss Deby. (Hoto: Christophe PETIT TESSON / POOL / AFP)
    Muhammad Aminu Ahmad

Kasar Faransa ta sake yin watsi da zarge-zargen cewa ta juya baya ga Mali ta hanyar janye dakarunta duk da halin da kasar ta yammacin Afirka take ciki a yanzu sakamakon tsanantar ayyukan ta’addanci.

Ma’aikatar Tsaron Faransa ce ta musanta zargin ta hanyar Kakakinta, Misis Anne-Claire Legendre.

Ta ce sauya fasali ko kuma salon tunkarar matsalolin tsaron da yankin Sahel yake fuskanta da kasar ta yi ba ya nufin ta janye daga Mali.

Karuwar zargin Faransa da kokarin janyewa daga Mali tana zuwa ne bayan da Firayi Ministan Kasar, Mista Choguel Kokalla Maiga ya ce uwar goyon nasu tana kokarin janyewa daga kasar a daidai lokacin da rikici yake tsananta ta hanyar rage yawan sojojinta da suke taimakawa a yaki da ta’addanci.

Mista Maiga ya ce abin takaici ne yadda Faransa take ci gaba da janye dakarunta daga Mali.

Sai dai Anne-Claire, ta nanata cewa Faransa ba ta da shirin janyewa daga Mali, maimakon haka tana son karfafa yakin da take yi da ’yan ta’adda a yankin na Sahel baki daya.

Ko a makon jiya, Ministar Tsaro ta Faransa, Misis Florence Parly ta musanta cewa kasar tana kokarin janyewa daga Mali dungurugum inda ta ce ko kadan Faransa ba ta da shirin juya baya ga Mali.

A watan Yunin da ya gabata ne Faransa ta fara rage yawan sojojinta da suke sansanin Kidal da Tumbuktu da kuma Tessalit yayin da ta bayyana shirin rage dakarun a yankin Sahel daga 5000 zuwa 2500 nan da shekarar 2023.