✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Tsawa ta hallaka jami’an Hukumar Kiyaye Hadurra uku

Tsawa ta yi ajalin wasu jami’an Hukumar Kiyaye Hadurra ta Kasa (FRSC) su uku a jihar Ogun. Jami’an da ibtila’in ya rutsa da su suna…

Tsawa ta yi ajalin wasu jami’an Hukumar Kiyaye Hadurra ta Kasa (FRSC) su uku a jihar Ogun.

Jami’an da ibtila’in ya rutsa da su suna bakin aiki ne lokacin da lamarin ya riske su ranar Laraba a yankin tsohuwar tollgate da ke karamar hukumar Ijebu-North East.

Mai magana da yawun hukumar a jihar ta Ogun, Florence Okpe, ta tabbatar da faruwar lamarin.

Lamarin dai ya auku ne a lokacin da jami’an ke cikin ofishinsu da ke yankin a daidai lokacin da suke shirin fitowa fareti da misalin karfe 10 na safe.

A lokacin da lamarin ya auku dai jami’an da ke wajen sun haura goma.