✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Tsawa ta hallaka mutum 3 a Katsina

Tsawa ta hallaka mutum uku cikin manoma biyar ‘yan gida daya da suka fake a karkashin wata bishiya yayin da ruwan sama mai karfi ke…

Tsawa ta hallaka mutum uku cikin manoma biyar ‘yan gida daya da suka fake a karkashin wata bishiya yayin da ruwan sama mai karfi ke sauka a kauyen Kukar-Gesa da ke karamar hukumar Kankara ta jihar Katsina.

Malam Musa Danladi, shi ne magidancin da ya tabbatar da mutuwar ‘ya‘yansa biyu da jikansa daya kuma ya jingina lamarin da kudira ta Ubangiji.

Wata majiya da ta fito daga cikin dangin mamatan, ta ce “ruwan saman ya fara sauka da misalin karfe 5.00 na Yammacin ranar Asabar, yayin da manoman biyar ‘yan gida daya suke girbin gero a gonarsu.

Majiyar a ranar Lahadi ta shaidawa manema labarai cewa, fadowar tsawar a kan bishiyar da manoman biyar suka fake a karkashinta ce ta yi sanadiyar mutuwar uku daga cikinsu yayin da ragowar biyun suka ji rauni.

Kamar yadda jaridar Vanguard ta ruwaito, an sanar da mutuwar mutanen uku bayan ruwan ya tsagaita da misalin karfe 11.00 na dare, sai dai an nemi gawawwakinsu an rasa.

Daga bisani an bazama wajen neman gawawwakin kuma cikin lokacin kankani aka samu nasara.

Bisa koyarwa ta addini Islama, an yi jana’izar mamatan da safiyar ranar Lahadi inda aka binne su a makabartar kauyen Kukar-Gesa.