✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Tserarrun fursunoni sun yi garkuwa da lauya mace a Fatakwal

Sun tsere daga kurkukun ne tun a watan Afrilun 2022

’Yan sanda a jihar Ribas sun sake kama wasu tserarrun fursunoni su biyu, bisa zargin su da yin garkuwa da wata lauya mace a Fatakwal, babban birnin jihar.

Rahotanni sun ce an sake kama Okechukwu Edison da Sunday Morison, ne bisa zargin su da yin garkuwar, duk da cewa dama ana neman su ruwa a jallo.

Dakarun sashen yaki da manyan laifuffuka na rundunar (FIB-IRT) ne suka kama su a Kwanar Rumuola da ke Fatakwal ranar 10 ga watan Nuwamban 2022.

Da yake tsokaci a kan lamarin ranar Lahadi, Kwamandan Rundunar ta IRT, Olatunji Disu, ya shaida wa ‘yan jarida a Abuja cewa mutanen biyu dama tsofaffin masu garkuwa ne, ’yan fashi kuma masu kwacen motoci.

Ya ce mutanen, wadanda ’yan asalin kauyen Rumuji ne na Karamar Hukumar Emuha ta jihar, sun shafe shekara 11 suna zaman jiran shari’a a kurkuku.

Olatunji ya kuma ce, “Sun shaida mana cewa sun tsere daga kurkukun ne tun ranar biyar ga watan Afrilun 2022, lokacin da wasu ’yan bindiga suka kai hari gidan suka saki fursunoni.

“Wadanda ake zargin tare da wasu mutum biyu da suka aikata laifin, sun shafe shekara 11 a baya a gidan yarin Owerri da ke jihar Imo, suna zaman jiran shari’a, kan zargin aikata garkuwa da mutane.

“Wadanda ake zargin, tare da wani mutum, wanda shi ma tsohon mai laifi ne daga gidan yarin sun shiga hannun ’yan sanda ne a Fatakwal bisa zargin garkuwa da wata lauya mace,” inji Olatunji.