✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Tsofaffi 3 sun yi wa kurma mai shekara 13 fyade a Zariya

Mutanen sun yi maa fyaden ne a wani gidan burodi

Ana zargin wani tsoho mai shekara 70 da wasu mutum biyu da yin fyade ga wata yarinya kurma mai kimanin shekara 13 da haihuwa a wani gidan burodi da ke Gangaren Kwadi a Tudun Wada, Zariya a jihar Kaduna.

Kurmar daliba ce ’yar aji shida na makarantar firamare, wacce tsofaffin suka yi ta mata fyade har zuwa lokacin da mahaifiyarta ta fara ganin wasu canje -canje a gabanta.

Wadanda ake zargin sune mai shekara 70 mais shekara 60 da kuma mai shekara 50 mazauna Gangaren kwadi da ke Tudun Wada a Zariyan.

Da yake tabbatar da faruwar al’amarin, Mai anguwar ta Gangaren Kwadi, Mallam Mohammed Danliti, ya ce bayan mahaifiyar Kurmar ta ga canji a gaban ‘yar ta ta, sa’ilin da take yawan cewa gabanta na ciwo, ta ce ta yi tsammanin ko keke ta hau ya haddasa mata da ciwon.

Ya kuma ce, “Sai daga baya da wata kawar kurmar ta sanar da mahaifiyar cewa tana ganin kurmar tana yawan zuwa gidan buredin ana ba ta kudi.

“Daga nan ne mahaifiyar ta dauko wuka ta kulle kurmar a daki ta yi mata kurarin za ta kashe ta in ba ta fada mata gaskiyar abin da ke faruwa ba.

“Nan ne kurma ta sanar da cewa mutanen suna yi mata fyade,” inji shi.

Mai Anguwar ya ci gaba da cewa daga nan ne mahaifiyar kurmar ta dauko wuka ta zo ta shake mai gidan burodin, tana kokarin daba mashi, a lokacin ne a ka kira shi, inda ya kai su ofishin ’yan sanda na Tudun Wada Zariya.

Ya ce yanzu dai duka mutum ukun suna hannun ’yan sanda inda ake ci gaba da gudanar da bincike a kansu.

Aminiya ta ziyarci Cibiyar Kula da Cin Zarafin Mata da Yara da ke asibitin Hajiya Gambo Sawaba Kofar Gayan inda aka kai yarinyar don likitoci su tabbatar da ko an yi mata fyaden, inda suka tabbatar da cewa tsofaffin sun lalata ta, kuma har sun shafa mata wani nau’in cuta.

Duk kokarin jin ta bakin Kakakin Rundunar ’Yan Sandar Jihar Kaduna, ya ci tura, saboda har zuwa lokacin hada wannan rahoton bai amsa rubutaccen sakon da wakilinmu ya aika masa ba.