✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Tsofaffin malaman makaranta sun yi zanga-zanga a Akwa Ibom

Tsofaffin malaman dai na zanga-zangar ne akan biyansu wasu hakkokinsu.

Tsofaffin malaman makaranta sun gudanar da zanga-zanga a Uyo, babban birnin Jihar Akwa Ibom saboda kin biyansu hakkokinsu.

Masu zanga-zangar sun toshe babbar titin IBB da ke cikin birnin na Uyo na tsawon sama da sa’a guda  tare da hana masu ababen hawa wucewa.

Suna dai kalubalantar gwamnati ne kan rashin biyansu hakkokinsu bayan kammala aiki tare da korafin a kara masu kudaden fansho.

Tsofaffin malaman sun kuma koka cewa ana biyan da dama daga cikinsu N2,000 ne kacal a matsayin fansho.

Sun rike kwalaye dauke da  rubuce-rubuce suna rokon Gwamnan Jihar da ya ceto rayuwarsu daga cikin halin da suka shiga, inda suka ce da yawa daga cikinsu ba sa iya cin abinci.

kwalayen na dauke da rubutu kamar ‘Ka ceci rayuwarmu, Udom Emmanuel’, ‘Ka Biya mu hakkokinmu’, ’Muna jin yunwa’, da sauransu.

Anyi yunkurin jin ta bakin hukumomin da abin ya shafa amma abin ya ci tura har zuwa lokacin hada wannan lokaci.