✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Tsohon Babban Hafsan Sojin Kasa zamanin mulkin Jonathan ya shiga APC

"Bayan shafe shekaru 38 a aikin soja, zai zama na yi asarar basirar da nake da ita in ban shiga siyasa ba."

Tsohon Babban Hafsan Sojin Kasa na Najeriya, Azubike Ihejirika ya shiga jam’iyyar APC mai mulki.

Ihejirika dai ya rike mukamin Babban Hafsan Sojin ne tsakanin shekarun 2010 zuwa 2014, zamanin tsohon Shugaban Kasa Goodluck Jonathan.

Ya shiga jam’iyyar ne a mazabarsa ta Ezere ta biyu a mazabar dan Majalisar Dattawa ta Abiya ta Kudu a jihar Abiya ranar Talata.

Ya yanki katin jam’iyyar ne a gaban Sanata mai wakiltar mazabar, Sanata Orji Uzor-Kalu.

Tsohon sojan ya ce ya yanke shawarar shiga jam’iyyar ne domin ya taimaka mata ta kai ga gaci a jihar Abiya da ma Najeriya baki daya.

A cewar Ihejirika, shekaru kusan 38 da ya shafe a aikin soja ya sanya ya sami dimbin basira da zai taimaka masa ya bayar da gudunmwa ga ci gaban Dimokradiyyar Najeriya.

Ya ce, “Na yanke shawarar cewa, bayan shafe shekaru 38 a aikin soja, zai zama kamar na yi asarar dimbin basirar da nake da ita ne idan ban shigo na bayar da gudunmawa a gwamnatance ba.

“Burina na farko bai wuce in ga na hada kan ’yan jam’iyyarmu ba, saboda hadin kai na da matukar muhimmanci,” inji shi.