✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto

Tsohon Babban Limamin Masallacin Quba ya rasu

Sheikh Muhammad Abid ya taba zama Limamin Sallar Tarawih a Masallacin Manzon Allah da ke Madinah.

Tsohon Babban Limamin Masallacin Quba, Sheikh Muhammad Abid, ya rasu.

Sheikh Muhammad Abid ya taba zama Limamin Sallar Tarawih ta Ramadanan shekarar 1410 bayan Hijirah, a Masallacin Manzon Allah da ke Madinah, tare da Marigayi Sheikh Muhammad Ayyub.

Sheikh Muhammad Abid

Masallacin Quba, shi ne masallaci na farko da aka gina a Madina a zamanin Manzon Allah Sallallahu alaihi Wasallama.