✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto

Tsohon da ake zargi da yi wa ’yar shekaru 2 fyade ya shiga hannu

Tsohon mai shekaru 63 ya yaudari yarinyar da Burodi yayin da ya mata fyaden.

’Yan sanda a jihar Edo sun cafke wani tsoho da ake zargi da yi wa yarinya ’yar shekaru biyu a duniya fyade.

Rundunar ’Yan Sandan ta jihar ce ta tabbatar da faruwar lamarin ta bakin kakakinta, Mista  Chidi Nwabuzor.

Chidi ya ce lamarin ya faru ne a yankin Urhonigbe dake Karamar Hukumar Orhionmwon dake jihar.

Ya ce tuni rundunar ta kammala bincikenta, kuma nan ba da jimawa ba za ta gurfanar da wanda ake zargin a gaban kotu.

Kamfanin Dillancin Labarai na Najeriya (NAN) ya rawaito cewa tsohon makocin gidan yarinyar da ake zargin ya yi wa fyaden ne.

Wanda ake zargin, ya yi amfani da Burodi wajen jan hankalin yarinyar zuwa dakinsa, wanda a nan ne ya yi amfani da damar wajen yin lalatar da ita.

Mahaifiyar yarinyar ce dai ta lura da abinda ya faru da yarinyar yayin da ta zo yi mata wanka.

Daga bisani bayan tsananta tambayoyi da mahaifiyar ta yi mata, yarinyar ta bayyana wa mahaifiyarta yadda tsohon ya yi mata fyaden.

Daga nan ne ita kuma mahaifiyar yarinyar ta garzaya ofishin ‘yan sanda na Abudu, wanda a nan ne ta shigar da kara kan lamarin.

Shugaban Kungiyar Dattawan jihar Edo, Mista Omogiade Edokpolor ya ce zai tsaya kai da fata wajen ganin an yi hukuncni da ya dace ga wanda ake zargin.

Omogiade ya ziyarci shalkwatar ‘yan sandan jihar a ranar Alhamis don nuna goyonsa ga iyayen yarinyar kan lamarin.