✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Tsohon dan sanda ya kashe mutum 34 da iyalansa a Thailand

Akalla mutum 34 aka rawaito sun mutu sakamakon harin da wani tsohon jami’in dan sanda ya kai a wata cibiyar rainon kananan yara a kasar…

Akalla mutum 34 aka rawaito sun mutu sakamakon harin da wani tsohon jami’in dan sanda ya kai a wata cibiyar rainon kananan yara a kasar Thailand.

Rahotanni sun ce maharin ya kashe iyalansa daga bisani ya kashen kansa bayan harin da ya kai wa cibiyar.

‘Yan sandan yankin sun ce wadanda suka mutu a harin sun hada da akalla kananan yara 22.

Bayanai sun ce an ga maharin dauke da bindiga da wuka, inda ya bude wuta a kan kananan yaran da sauran mutane a cibiyar rainon da ke yankin Nong Bua Lamphu da misalin karfe 12:30 na ranar Alhamis.

Shaidu sun ce da karfin tsiya maharin ya kutsa dakin da yaran suke kwance inda kai-tsaye ya bude musu wuta suna tsakar barci.

Sun kara da cewa, bayan kai harin ne kuma ya nufi gidansa, inda ya kashe matarsa da dansu daya kafin daga bisani ya kashe kansa.